1 Agusta 2023 - 08:02
Jami'an tsaron gwamnatin Sahayoniya: Ba ma son mu yi arangama da Hizbullah

Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun ruwaito a safiyar jiya litinin cewa jami'an tsaron wannan gwamnati sun bayyana a taron tsaro na majalisar ministocin Benjamin Netanyahu cewa ba sa son fuskantar yaki da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, An gudanar da taron tsaro na majalisar ministocin yahudawan sahyoniya dangane da abubuwan da ke faruwa a yankin arewacin Palastinu da ta mamaye.

Jaridar "Yediot Aharonot" ta harshen Hebrew ta rubuta cewa Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tantance yanayin tsaro a arewacin Falasdinu da ta mamaye a shekaran jiya Lahadi.